(Babbar riga jappa hula)
Indai zallar al'adace jeku gurun Hausawa
Kyawun tarbiyya alkunya babu kamarmu arewa
Karin magana ga iya zance kai har tarin baiwa
Kome yashigo zamani zakuga dai bama kasawa
Afagen ilimii bama raina karatu boko islmaa, tuni dai tarihi munyi kafawa
Tarin al'umma kai malam sai kazo kayi ganewaa
Turban najeriya dagananne Sardauna tafawaɓalewa
(Babbar riga jampa hula) shigar alfarmace
Kusani al adatace
Ai wankan girmane
Banda shigar data zarcemin wannan
Toh dazarar munkoma fannin sana'o'ii ba abarmu abayaba
Mukejan ragamar kasuwanci tsoho yaro babba
Muke sana'ar wanzanci Kiwo Noma bashi kenanba
Ƙira Jima Fawa Saƙa da Rini da Kitso duka bawaiba
Dukanci Sussuka Arkomanci da Gini kumuyo duba
Farautaa Sassaƙaa Gininn Tukwane Su ba'akaiy muba
Nagano indai ɗinkin kayan sawane ba'azarce muba
Anshaka masilla duk saurayin dabaisa Babbar rigabaa